Gaisuwa ta musamman
16Yanzu, bari Ubangiji mai salama kansa yă ba ku salama a kowane lokaci da kuma a ta kowace hanya. Ubangiji yă kasance tare da ku duka.
17Ni, Bulus, nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna, wannan ce shaida a kowace wasiƙata, haka nake rubutu.
18Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ku duka.


