Habakkuk ya nuna damuwa

2Har yaushe, ya Ubangiji, zan yi kukan neman taimako,

amma ka ƙi ji?

Ina kuka a gare ka saboda zalunci

amma ba ka ce ufam ba.

3Me ya sa ka bari ina ta kallon rashin gaskiya?

Me ya sa kake barin abin da ba daidai ba?

Hallaka da tashin hankali suna a gabana;

ga rashin jituwa da faɗa ko’ina.

4Saboda haka ba a bin doka,

shari’a kuma ba ta aiki.

Mugaye sun kewaye masu adalci

don a hana gaskiya tă yi aiki.