Dutsen Ubangiji
1Ga abin da Ishaya ɗan Amoz ya gani game da Yahuda da Urushalima.
2A kwanaki masu zuwa
za a kafa dutsen haikalin Ubangiji
a matsayin babba cikin duwatsu;
za a daga shi bisa tuddai,
kuma dukan al’ummai za su bumbunto zuwa gare shi.
3Mutane da yawa za su zo su ce,
“Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji,
zuwa gidan Allah na Yaƙub.
Zai koya mana hanyoyinsa,
domin mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.”
Dokar za tă fito daga Sihiyona,
maganar Ubangiji daga Urushalima.
4Zai shari’anta tsakanin al’ummai
zai kuma sulhunta faɗar mutane masu yawa.
Za su mai da takubansu su zama garemani
māsunsu su zama wuƙaƙen askin itatuwa.
Al’umma ba za tă ƙara ɗauki takobi a kan al’umma ba,
ba kuwa za su ƙara yin horarwar yaƙi.
5Ki zo, ya gidan Yaƙub,
bari mu yi tafiya a hasken Ubangiji.


