Kaito da hukunce-hukunce
8Kaitonku ku waɗanda kuke ƙara wa kanku gidaje
kuke kuma haɗa gonaki da gonaki
har babu sauran filin da ya rage
ku kuma zauna ku kaɗai a ƙasar.
9Ubangiji Maɗaukaki ya furta a kunnuwana,
“Tabbatacce manyan gidajen za su zama kango,
za a bar kyawawan gidajen nan ba kowa.
10Kadada goma na gonar inabi zai ba da garwan ruwan inabi ɗaya kaɗai,
mudu guda na iri kuma zai ba da efa na hatsi guda kurum.”
11Kaiton waɗanda suke tashi da sassafe
don su nufi wurin shaye-shaye,
waɗanda suke raba dare
har sai sun bugu da ruwan inabi.
12Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu,
ganguna da busa da ruwan inabi,
amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba,
ba sa biyayya ga aikin hannuwansa.
13Saboda haka mutanena za su yi zaman bauta
domin rashin fahimi;
manyan mutanensu za su mutu da yunwa
talakawansu kuma su mutu da ƙishirwa.
14Saboda haka kabari ya fadada marmarinsa
ya kuma buɗe bakinsa babu iyaka;
cikinsa manyan mutanensu da talakawansu za su gangara
tare da dukan masu hayaniyarsu da masu murnansu.
15Ta haka za a ƙasƙantar da mutum
kuma za a ƙasƙantar da ’yan adam,
za a ƙasƙanta da masu girman kai.
16Amma Ubangiji Maɗaukaki zai sami ɗaukaka ta wurin aikata gaskiya,
kuma Allah mai tsarki zai nuna kansa ta wurin adalcinsa.
17Sa’an nan tumaki za su yi kiwo kamar yadda suke yi a wurin kiwonsu;
raguna za su yi kiwo cikin abubuwa masu kyau da suka lalace.
18Kaiton waɗanda suke jan zunubi da igiyar ruɗu,
da kuma mugunta da igiyoyin keken yaƙin,
19waɗanda suke cewa, “Bari Allah yă gaggauta,
bari yă hanzarta aikinsa
don mu gani.
Bari yă iso,
bari shirin Mai Tsarkin nan na Isra’ila yă zo,
don mu sani.”
20Kaiton waɗanda suke ce da mugunta nagarta
nagarta kuma mugunta,
waɗanda suke mai da duhu haske
haske kuma duhu,
waɗanda suke mai da ɗaci zaƙi
zaƙi kuma ɗaci.
21Kaiton waɗanda suke tsammani suna da hikima
da kuma wayo a idonsu.
22Kaiton waɗanda suke jarumawa a shan ruwan inabi
da gwanaye a haɗin abubuwan sha,
23waɗanda suke ƙyale masu laifi don sun ba da cin hanci,
amma su hana a yi gaskiya wa marasa laifi.
24Saboda haka kamar yadda harshen wuta yakan lashe kara
kuma kamar yadda busasshiyar ciyawa takan ƙone ƙurmus a cikin wuta,
haka saiwarsu za su ruɓa
iska kuma ta hura furanninsu kamar ƙura;
gama sun ƙi dokar Ubangiji Maɗaukaki
suka kuma ƙyale maganar Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
25Saboda haka fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan mutanensa;
ya ɗaga hannunsa ya kuma buge su.
Duwatsu sun jijjigu,
gawawwaki kuwa suka zama kamar juji a tituna.
Saboda wannan duka, fushinsa bai huce ba,
bai kuwa janye hannunsa ba.
26Ya ɗaga tuta don al’ummai masu nisa,
ya yi feɗuwa wa waɗanda suke a iyakar duniya.
Ga shi sun iso,
da sauri da kuma gaggawa!
27Babu ko ɗayansu da ya gaji ko ya yi tuntuɓe,
babu ko ɗaya da ya yi gyangyaɗi ko barci;
babu abin ɗamarar da ya kunce a gindi,
ba igiyar takalmin da ta tsinke.
28Kibiyoyinsu masu tsini ne,
an ɗaura dukan bakkunansu;
kofatan dawakansu sun yi kamar dutsen ƙanƙara,
ƙafafun keken yaƙinsu kamar guguwa ne.
29Rurinsu ya yi kamar na zaki,
suna ruri kamar ’yan zakoki;
suna yin gurnani yayinda suke kamun abin da suke farauta
su ɗauke shi ba mai ƙwace shi.
30A wannan rana za su yi ta ruri a kansa
kamar rurin teku.
Kuma in wani ya dubi ƙasar,
zai ga duhu da damuwa;
haske ma zai zama duhu ta wurin gizagizai.


