An ƙaunaci Yaƙub, aka ƙi Isuwa
2“Na ƙaunace ku, in ji Ubangiji.
“Amma sai kuka ce, ‘Yaya ka ƙaunace mu?’
“Isuwa ba ɗan’uwan Yaƙub ba ne?” In ji Ubangiji. “Duk da haka na ƙaunaci Yaƙub, 3amma na ƙi Isuwa, na kuma mai da ƙasarsa da take kan duwatsu kango, na ba da gādonsa ga dilolin hamada.”
4Edom zai iya cewa, “Ko da yake an ragargaza mu, ai, za mu sāke gina kufanmu.”
Amma ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Za su iya gini, amma zan rushe. Za a ce da su Muguwar Ƙasa, mutane da kullum suke a ƙarƙashi fushin Ubangiji. 5Za ku ga wannan da idanunku ku kuma ce, ‘Ubangiji da girma yake, har gaba da iyakokin Isra’ila ma!’


