Select a Verse

Mulkin adalci

1Duba, sarki zai yi mulki cikin adalci

masu mulki kuma su yi mulki da adalci.

2Kowane mutum zai zama kamar wurin fakewa daga iska

mafaka kuma daga hadari,

kamar rafuffukan ruwa a hamada

da kuma inuwar babban dutse a ƙeƙasasshiyar ƙasa.

3Sa’an nan idanun waɗanda suka gani ba za su ƙara rufewa ba,

kunnuwan waɗanda suka ji kuma za su saurara.

4Zuciya marasa haƙuri za su sani su kuma fahimta,

harshen masu ana’ana kuma zai sāke su yi magana sosai.

5Ba za a ƙara ce da wawa mai girma ba

ko kuwa a ɗaukaka mazambaci.

6Gama wawa maganar wauta yakan yi,

zuciyarsa ta cika da mugunta,

yana aikata abubuwan rashin sanin Allah

yana baza kurakurai game da Ubangiji;

yana barin mayunwata da yunwa

ya kuma hana masu ƙishirwa ruwan sha.

7Matakan mazambaci mugaye ne,

yana ƙulla mugayen shirye-shirye

don yă hallaka talakawa da ƙarairayi,

ko sa’ad da roƙon mai bukata da gaskiya ne.

8Amma mutumin kirki kan yi shirye-shirye masu kirki,

kuma yakan tsaya a kan ayyukan kirki.

Matan Urushalima

9Ku matan da kuke zaman jin daɗi,

ku tashi ku saurare ni;

ku ’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya,

ku ji abin da zan faɗa!

10Cikin ɗan lokaci ƙasa da shekara guda

ku da kuke tsammani kuna da kāriya za ku yi rawar jiki;

girbin ’ya’yan inabi zai kāsa,

girbin ’ya’yan itatuwa kuma ba zai zo ba.

11Ku yi rawar jiki, ku mata masu jin daɗi,

ku sha wahala, ku ’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya!

Ku tuɓe rigunanku,

ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.

12Ku bugi ƙirjinku don gonaki masu kyau

don ’ya’yan inabi

13da kuma don ƙasar mutanena,

da ƙasar da ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya ne suka yi girma,

I, ku yi kuka saboda dukan gidajen da dā ake biki

da kuma domin wannan birnin da dā ake murna a ciki.

14Za a ƙyale kagarar,

a gudu a bar birnin da dā ake hayaniya;

mafaka da hasumiyar tsaro za su zama kango har abada,

jin daɗin jakuna, makiyaya don garkuna,

15sai an zubo Ruhu a kanmu daga sama,

hamada kuma ta zama ƙasar mai taƙi,

gona mai taƙi kuma ta zama kamar kurmi.

16Aikin gaskiya zai zauna a hamada

adalci kuma zai zauna a ƙasa mai taƙi.

17Aikin adalci zai zama salama;

tasirin adalci zai zama natsuwa da tabbaci har abada.

18Mutanena za su zauna lafiya a wuraren salama,

a gidaje masu kāriya,

a wuraren hutun da babu fitina.

19Ko da yake ƙanƙara za tă fāɗo a jeji,

a kuma rurrushe birni gaba ɗaya,

20zai zama muku da albarka,

ku da kuke shuki iri kusa da kowane rafi,

kuna kuma barin lafiyayyiyar makiyaya domin shanu da jakunanku.