Select a Verse

Aikin Ishaya

1A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali. 2A bisansa akwai serafofi, kowanne yana da fikafikai shida. Fikafikai biyu sun rufe fuskokinsu, da biyu suka rufe ƙafafunsu, biyu kuma da su suke tashi. 3Suna kiran juna,

“Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne;

duniya ta cika da ɗaukakarsa.”

4Da jin ƙarar muryoyinsu madogarai da madogaran ƙofa suka girgiza, haikali kuma ya cika da hayaƙi.

5Sai na tā da murya na ce, “Kaitona! Na shiga uku! Gama ni mutum ne mai leɓuna marar tsarki, kuma ina raye a cikin mutane masu leɓuna marasa tsarki, idanuna kuma sun ga Sarki, Ubangiji Maɗaukaki.”

6Sai ɗaya daga cikin serafofin ya yi firiya zuwa wurina tare da garwashi mai wuta a hannunsa, wanda ya ɗiba da arautaki daga bagade. 7Da shi ne ya taɓa bakina ya ce, “Duba, wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.”

8Sa’an nan na ji muryar Ubangiji tana cewa, “Wa zan aika? Wa zai tafi mana?”

Sai na ce, “Ga ni! Ka aike ni!”

9Ya ce, “Je ka ka faɗa wa wannan mutane,

“ ‘Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba;

Kome yawan dubar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.’

10Ka sa zuciyar mutanen nan ta dushe;

kunnuwansu su kurunce,

idanunsu kuma su makance.

In ba haka ba za su iya gani da idanunsu,

su ji da kunnuwansu,

su fahimta da zuciyarsu,

su kuma juyo a kuma warkar da su.”

11Sa’an nan na ce, “Har yaushe, ya Ubangiji?”

Ya kuma amsa,

“Sai an lalatar da biranen

ba kowa a ciki,

sai an mai da gidaje kangwaye

ƙasa kuma ta zama kango ba amfani,

12sai lokacin da Ubangiji ya kori kowa

aka kuma yashe ƙasar gaba ɗaya.

13Ko da yake kashi ɗaya bisa goma zai ragu a ƙasar,

za tă sāke zama kango.

Amma kamar yadda katambiri da itacen oak

sukan bar kututturai sa’ad da aka yanke su,

haka iri mai tsarkin nan zai zama kututture a ƙasar mai tsarki.”