Select a Verse

Zabura 3

Zabura ta Dawuda. Sa’ad da ya gudu daga ɗansa Absalom.

1Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne!

Su nawa suke gāba da ni!

2Da yawa suna magana a kaina suna cewa,

“Allah ba zai cece shi ba.” Sela

3Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji;

ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.

4Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi,

ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela

5Na kwanta na yi barci;

na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.

6Ba zan ji tsoro ko dubu goma

suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.

7Ka tashi Ya Ubangiji!

Ka cece ni, ya Allahna!

Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi;

ka kakkarya haƙoran mugaye.

8Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo.

Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Sela